Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Da yake ishara game da ziyarar da Rafeel Grossi shugaban hukumar ta IAEA ya kawo nan Iran a yau litinin, KhadibZadeh ya kara da cewa yana fatan ziyarar ta zama mai ma’ana kamar ta bayanta.
Ya ce a kowanne lokaci muna shawartar hukumar ta tsaya a bangaren da ya shafi kayan aiki ka da ta bari wasu kasashe su yi amfani da sunanta don cimma manufofin siyasa da manufofin kashin kai.
Daga karshe ya ce Iran da sauran kasashen da ake tattaunawa kan shirin nukiliyarta suna bukatar samun tabbaci daga bangaren Amurka a Taron Biyanna da za’a yi a ranar 29 ga watan nuwamba ,ka da tarihi ya sake maimaita kansa ta yi abin da tsohon shugaban kasar Donlad Trumph yayi na ficewar daga yarjejeniyar a shekara ta 2015.
342/